Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci ta sama da ta kasa kan Falasdinawa

Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci ta sama da ta kasa kan Falasdinawa

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci ta sama da ta kasa kan yankin Zirin Gaza dake karkashin mamaya tsawon shekaru.

Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai ta sama da ta ruwa a lokaci guda zuwa arewa maso-gabas da arewa maso-yammacin Zirin Gaza.

Sakamakon hare-haren an samu katsewar lantarki a yankunan, an kuma hango gobara ta kama a yankunan.

An kai motocin daukar marasa lafiya da jami'an kula da lafiya zuwa yankunan.

Ofishin Yada Labarai na Rundunar Sojin Isra'ila game da batun ko sojojin sun shiga Gaza, ya bayyana cewa, "Ba za mu iya tabbatar da ko sun shiga ba ko kuwa ba su shiga ba."

Kakakin Rundunar Sojin Isra'ila Jonathan Conricust ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, sun fara kai hare-hare ta kasa a Zirin Gaza.

Amma wata sanarwa da aka sake fitarwa daga ofishin ta ce, an samu matsala wajen fassara, ba a fara kai hare-hare ta kasa ba.

Ya zuwa yanzu Falasdinawa 103 da suka hada da yara kanana 27 ne suka yi Shahada sakamakon hare-haren ta'addanci da Isra'ila ta fara kai musu a ranar 10 ga watan Mayu kuma cikin Azumin watan Ramadhan.


News Source:   ()