'Yan sandan Isra'ila sun kai hari kan Falasdinawa a yankin tsohon garin Gabashin Kudus da unguwannin Kofar Sham da Shaikh Jarrah.
'Yan sandan na Isra'ila sun kai hari kan Falasdinawan da suka taru don yin Sallah a Masallacin Aksa, sannan sun tarwatsa wasu da suka taru don yin zanga-zanga a unguwar Kofar SHam.
A unguwar Shaikh Jarrah kuma 'yan sandan na Isra'ila sun kaiwa Falasdinawan da ake kora daga gidajensu hari.
Sanarwar da Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent ta fitar ta bayyana cewa, 'yan sandan Isra'ila sun harba harsashan roba da bama-bamai masu kara kan Falasdinawa a unguwannin Kofar Sham da Shaikh Jarrah.
Sanarwar ta ce Falasdinawa 18 sun jikkata sakamakon hare-haren na Isra'ila.
Ya zuwa yanzu sama da Falasdinawa 65 da suka hada da mata 5 da yara kanana 16 ne suka yi Shahada sakamakon hare-haren zalunci da dakarun Isra'ila ke kai musu.