An tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun yi amfani da muggan makamai wajen dakatar da zanga-zangar Falasdinawa lamarin dake sanadiyyar mutuwar yara.
Kungiyar Kare Yara ta Kasa da Kasa da ke Geneva ta sanar da cewa sojojin Isra’ila sun yi amfani da makamin da aka fi sani da “Ruger mai kisa” da ake kira “22 Long Rifle” lamarin da ya yi sanadiyar rayukan yara.
Kasancewar amfani da ire-iren miyagun makaman da suke yi, a ranar 4 ga watan Disamba ma wani matashin Bafalasdine dan shekara 13 mai suna Ali Abu Aliyya ya ras ransa a Zirrin Gaza.
Isra'ila dai na ikirarin cewa ba ta yi amfani da muggan makamai ba.
Dangane ga alkaluman kungiyoyin lauyoyi na kasa da kasa, tun daga farkon wannan shekarar, yaran Falasdinawa 8 ‘yan shekaru tsakanin 13 zuwa 17 sun yi shahada sakamakon bude wuta da sojojin Isra’ila suka yi.