Iran ta zargi Isra'ila da kashe Fahrizade ta kuma sha alwashin mayar da martani

Iran ta zargi Isra'ila da kashe Fahrizade ta kuma sha alwashin mayar da martani

Shugaba kasar Iran Hassan Rouhani ya ce kisan Fahrizade, wanda ya kirkiro shirin nukiliyar Iran tarkon Isra’ila ne kuma za a ba da amsa a lokacin da ya dace.

Ya kara da cewa, makiyan Iran sun sani sarai al'ummar Iran da shugabaninsu sun nuna jarunta kuma sun kuduri aniyar ba da amsar wannan kisan. Hukumomin da abin ya shafa za su mayar da martani kan wannan laifin a lokacin da ya dace. Mutanenmu suna da hikimar da ba zasu fada cikin tarkon gwamnatin Yahudawa ba. 

Shugaban addinin kasar Iran Ali Hamaney ya yi kira ga hukumomin kasar da su bi sawon kashe masanin kimiyyar kasar Muhsin Fahrizade.

Ali Hammaney ya fitar da sanarwa a rubuce game da kashe masanin kimiyyar fasahar nukiliyar kasar Muhsin Fahrizade inda yake cewa,

"Kashe Fahrizade bakar anniya ce wanda aka aikata ta hanyar "hayar masu kashe mutane" wadanda suka kasance azzalumai."

Ya zama wajibi abi sawon wannan aika-aika sau da kafa domin kama azzaluman da kuma hukuntasu. Ya kuma zama wajibi asan da cewa dukkanin ayyukan da Fahrizade ya fara dole a cigaba dasu.

 


News Source:   ()