Ministan Harkokin Wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa ya kamata dukkan kasashe su yi aiki tare don rarraba sabbin nau'in allurar rigakafin coronavirus (Covid-19), sannan ya zargi Amurka da cewa tana tanadar rigakafin fiye da yadda take bukata.
Zarif, a cikin sakon da ya yada a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa,
"Ya kamata a mayar da martani game da barkewar cutar Covid-19 a duniya ta hanyar inganta rarraba allurar rigakafin bisa tsari."
Zarif ya ce, kasashe da dama, musamman Falasdinawa, sun tilastu da su dogara da kansu a cikin annobar Korona saboda bakar takunkumin da aka kakkabawa Iran don Isra’ila.
"Amurka na da rarar alluran rigakafin Korona. Tanadar allurar rigakafin Korona fiye da yadda kasa ke bukata kisan gilla ne."