Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Musevi ya bayyana cewa kasar Iran ta yi matukar farin cikin sake mayar da Hagia Sophia Masallaci domin sake fara ibada a cikinsa.
Musevi, ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu da cewa,
"Matakin da Turkawa da Musulmin duniya suka yi farin ciki tare da yin maraba dashi muma mun kasance cikin farin ciki sakamakon sake mayar da Hagia Sophia Masallaci"
A yayin da yake sharhi akan wasu kasashe da suka kalubalanci matakin Musevi ya bayyana cewa,
"Maslahar Hagia Sophia maslahar cikin gidan Turkiyya ne. Wannan mataki ne da ya ta'alaka ga 'yancin Turkiyya ita kadai tilo"