Iran ta yi farin cikin dakatar da baiwa Saudiyya tallafin yaki a Yemen

Iran ta yi farin cikin dakatar da baiwa Saudiyya tallafin yaki a Yemen

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Said Hatibzade ya bayyana cewa matakin da Amurka ta dauka na dakatar da tallafin da take baiwa Saudiyya akan yaki da take yi a Yemen "matakin da Amurkan za ta gyara kuskurenta."

Hatibzade ya bayyana cewa ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi farin cikin matakin da Amurka ta dauka akan Yemen. Inda ya kara da cewa,

"Idan har shawarar dakatar da goyon baya ga kawancen Saudiyya da kuma rashin sayar da makamai ba dabara ce ta siyasa ba, zai iya zama mataki na gyara kurakuran da suka gabata."

A yayinda Hatibzade ke bayyana cewa Iran na matukar farin cikin dakatar da gudunmowar sajin da Amurka ke baiwa Saudiyya a yakin Yemen, inda ya kara da cewa hakan ba zai wadata ba sabili da haka yana kira ga sauran kasashen dake baiwa Saudiyya taimako a kan hakan su ma su dakatar.

 


News Source:   ()