A kasar Iran an yankewa wasu ma'aurata hukuncin kisa bayan kamasu da laifiun cin hanci da rashawa, zamba cikin aminci a kasuwar hada-hadar canji da makamantansu.
Kanfanin Dillancin Labaran Kasar Iran ta IRNA ta rawaioto cewa mai magana da yawun Alkali Erki Gulam Hüseyin Ismaili ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Tehran, babban birnin kasar.
Ma'auracin Wahid Behzadi da matarsa Nejwa Lashidayi an yanke musu hukuncin kisa bayan an samesu da laifin zamba cikin aminci, fasakwauri a kasuwar hada-hadar canji. cin hanci da rashawa a siyar da motoci kwara dubu 6 da 700 da kuma samunsu da tsabar kudade har na dubu 24 da 700 da kuma kilo daya na gwal.
Isma'il ya bayyana cewar suna damar su daukaka kara inda ya kara da cewa an kuma yankewa wasu 'yan majalisu daurin watanni 61 a gidan yari bayan su ma an kamasu da aikata laifin cin hanci da rashawa.