Bayan karuwar rikice-rikice a Afganistan, Iran ta rufe ƙofar kan iyaka da ƙasar a lardin Sistan-Baluchestan.
Dangane da labarin kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA, arangama tsakanin 'yan Taliban da dakarun gwamnati ya karu a kusa da birnin Zerenc a lardin Nimruz, a kan iyaka da Iran.
Bayan hakan aka rufe Kofar Iyaka ta Milak da ke kan iyakarta da Afganistan.
Mataimakin gwamnan lardin Sistan-Baluchestan, Mohammad Hadi Mareshi a jiya ya ce 'yan Taliban sun kwace birnin Zaranj da ke Afganistan, amma Taliban ta janye bayan mayar da martani da sojojin gwamnati suka yi.
Mereshi ya bayyana cewa an rufe Kofar Iyaka ta Milak saboda karuwar rikice-rikice kuma an dawo da manyan motoci 270 dake hanyar zuwa Afganistan daga Iran.