Iran ta karyata kafafen labaran kasashen waje

Iran ta karyata kafafen labaran kasashen waje

Shugaban hafsan sojojin kasar Iran ya karyata ikirarin da ake yi na wai hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Siriya a 'yan shekarun  da suka gabata ta kashe dubban sojojin Iran inda ya kara da cewa sojojin Iran 8 ne kawai suka rigamu gidan gaskiya.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Iran janar Ebulfazl Şikarçi, ya karyata shaci- fadin da ake yi na wai Isra'ila ta kashe sojojin Iran da dama a harin da take kaiwa a Siriya a 'yan shekarun nan.

Janar Şikarçi ya bayyana cewa a hare-haren da Isra'ila ta kai Siriya sojojin Iran 8 ne kachal suka rasa rayukansu.

Isra'ila da ta fara kai hare-hare a yankunan da sojojin Iran suke tun bayan barkewar yakin basasa a Siriya a shekarar 2011 ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a 'yan kwanakin nan.

A halin yanzu kafafen yada labaran kasashen waje na ikirarin cewa Isra'ila ta kashe sojojin Iran da dama da kuma wasu mayakan da keda alaka da ita.

 


News Source:   www.trt.net.tr