An sanar da cewa a garin Erdebil dake ķasar lran inda mafi yawan Turkawa ke zama an gudanar da zanga- zangar domin nuna goyon baya ga yankin Nagorno Karabakh dake karkashin mamayar Armenia.
A zanga zangar jami'an tsaro sun kame mutum 11.
Hukumar kare hakkin bil adama a ķasar lran ta (HRANA) ta fuskanci kalubale daga jami'an tsaro wadanda suka yi yunkurin tarwatsasu da barkonon tsohowa yayinda suke gudanar da zanga zanga nuna goyon baya ga yankin Nagorno Karabakh dake karkashin mamayar Armenia.
Baya ga kame masu fafutukan kare hakkin bil adama a zanga zangar mutum uku daga cikinsu sun raunana.
Masu fafutukan kare hakkin bil adama na ci gaba da kira da a gudanar da zanga zanga nuna goyon baya ga yankin Nagorno Karabakh dake karkashin mamayar Armenia a biranen Erdebil, Tebriz da Urumiye a kasar lran.