A Iran an sanar tsare mutane 320 da ake zargin sun yi rubuce-rubucen karya wadanda suka tayar da hankalin al'umma game da sabon nau'in cutar coronavirus (Covid-19).
Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labaran Iran (ILNA), Kwamandan rundunar ‘yan sandan Iran Janar Hüseyin Eşteri, ya bayyana cewa wadannan mutanen sun dinga yada jita-jita ta shafukan sadar da zumunta inda ya kara da cewa,
"An tsare mutane 320 wadanda suka yada labaran shaci-fadi masu tayar da hankali game da barkewar cutar Covid-19 a kafofin sada zumunta."
Annobar cutar corona da ta bulla a China ta bayyana a kasar Iran a jihar Kum a ranar 19 ga watan Febrairu.
Kawo yanzu dai cutar ta yi ajalin mutane dubu 6 da dari 640 a fadin kasar na Iran.