A wata sanarwa da rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar, ta ce harin na Iran martani ne game da kisan jagoran ƙungiyar Hamas Isma’il Haniyeh, da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai birnin Tehran a watan Yulin wannan shekarar.
Iran ta ce harin makamai masu linzami da ta kai Isra'ila, shi ne mafi girma da ta taba kaiwa ƙasar, wanda ya kara haifar da fargabar barkewar yaki a yankin Gabas ta tsakiya.
Rundunar sojojin Iran ta yi gargadin cewa, duk wata ƙasa da ta yi yunkurin taimakawa Isra’ila kai tsaye, za ta dandana kudarta.
A wata ganawa da aka yi da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi a kafar Talabijin din ƙasar, ya ce Tehran ta gargadi Amurka game da tsoma baki bayan harin da ta kai kan Isra'ila.
Mun gargadin sojojin Amurka da su janye daga wannan lamari, kada su sanya kansu a ciki.
Abbas ya ce sun mikawa Amurka sakon ne ta ofishin jakadancin ƙasar Switzerland da ke Tehran.
Bayan wannan hari, mutane da dama ne suka taru a biranen Tehran da Beirut da Baghdad da Gabar Yammacin kogin Jordan da kuma Gaza, inda suke murna ta hanyar daga tutocin Hezbollah da Lebanon da kuma Iran.
Tuni dai ƙasashen Amurka da Spain da Jamus da Faransa da Birtaniya da Japan suka yi Allah wadai da harin na Iran kan Isra’ila, inda Spain da Jamus ke bukatar kawo ƙarshen rikicin.
Wasu daga cikin tankokin yakin Isra'ila a iyakar Lebanon, a ranar 1 ga watan Oktoba 2024. AP - Baz RatnerSai dai har yanzu ana ci gaba da gwabza rikici tsakanin Isra’ila da Hezbollah a iyakar Lebanon, inda ƙungiyar Hezbollah ta ce ta yi arangama da sojojin Isra'ila da suka yi kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon ta kasa, tare da kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kan iyakar ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar a safiyar Laraban nan, Hezbollah ta ce ta yi amfani da rokoki da makaman atilari wajen kaiwa wasu sansanonin Isra’ila hari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI