Kafar yada labaran Associated Press (AP) ta rawaito cewa kasar Iran ta fara ayyukan bunkasa harkokin nukiliya a karkashin kasa a yankin Fordo.
Iran dai bata fito fili ta bayyana ko tana aikin harkokin nukliya a karkashin kasa ba, gabanin kasashen yamma su gano a 2009 lamarin da ya haifar da yarjejeniyar nukiliya da Tehran a shekarar 2015.
Duk da yake dai ba a tabbatar da manufar ginin da aka fara ginawa ba, ayyukan da kasar ke yi a Fordo zai haifar da sabbin damuwa gabanin Trump ya bar ofis.
Iran dai ta na wani ginin ayyukan nukiliya a Natanz bayan fashewar wani abu da aka samu a watan Yuli abinda Tehran ta bayyana a matsayin kutin gwila.