Jakada Kazim Garib Abadi, Wakilin din-din-din na Iran a Majalisar Dinkin Duniya (UN) Ofishin Vienna ya ce, an fara aikin bincike don samar da wani nau'in mai da za a yi amfani da a injin makamashin nukiliya na Iran.
Jakada Abadi ya fitar da wata sanarwa ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce an sanar da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) game da samar da man.
Ya kara da cewa “a matakin farko, za a yi amfani da ma’adanin uranium don samar da karfen uranium."
A gefe guda kuma, Tsarin Hadin Gwiwa (KOEP), wanda aka sanya hannu a kai a shekarar 2015 kuma aka fi sani da yarjejeniyar nukiliya ta Iran, ba ya ba Iran damar yin bincike da ci gaba a kan ma’adinan plutonium ko uranium.
Masana na daukar karfen uranium a matsayin batu da ya kamata a yi nazari a kai, tunda ana amfani da shi ne wajen kera makaman nukiliya.