Da misalin ƙarfe 8 na yamma agogon Isra’ila ne makaman na Iran suka fara sauka akan birnin Tel Aviv, mintuna kaɗan bayan da Isra’ila ta Amurka suka buƙaci mazauna birnin na Tel Aviv da su nemi mafaka saboda suna da tabbacin cewa Iran na shirin ƙaddamar da farmakin.
Mafi yawan makaman da Iran ta harba Isra’ila ta yi nasarar kakkaɓo su, yayin da wasu suka fada a cikin birnin.
Amurka da Jordan sun taimaka wa Isra’ila kakkaɓo makamai
Sanarwa daga fadar gwamnatin Amurka (White House) ta ce tuni shugaba Joe Biden ya bai wa dakarunsu umurnin taimaka wa Isra’ila wajen kakkaɓo makaman da Iran ke cillawa.
Ita ma ƙasar Jordan wadda ke maƙotaka da Isra’ila, ta ce dakarunta sun yi nasarar lalata wasu daga cikin makaman da Iran ta harba, inda ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne domin kare sararin samaniyarta.
Isra’ila na shirin mayar da zazzafan martani kan Iran
Tuni dai Isra’ila ta bakin mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar Rear Admiral Daniel Hagari, ta ce za ta mayar wa Iran martani a lokacin da ya dace, inda ya ƙara da cewa yanzu haka suna shiri na musamman domin Iran.
Ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a Iraki kuma suke mara wa Iran baya, sun ce matukar wata ƙasa ta kai wa Iran hari, to nan take za su ƙaddamar da hare-hare kan muradun Amurka.
Ƙasashe da dama sun rufe sararin samaniyarsu
Jim kaɗan bayan da ƙaddamar da wannan farmaki ne Isra’ila ta sanar da rufe sararin samaniyarta, wanda hakan zai bai wa jami’an tsaronta cikakkiyar damar tantance makamin da ke zuwa da abokan gaba.
Ita ma Libanan wadda ke maƙotaka da Isra’ila ta ɓangaren arewa, ta ɗauki irin wannan mataki na rufe sararin samaniyarta, kamar dai yadda Iraki ta rufe nata sararin samaniyar, yayin da mahukunta a Iran suka bayar da umurnin rufe filin sauka da tashin jiragen saman birnin Tehran a cikin gaggawa.
Ƙasashen duniya na nuna fargaba a game da wannan sabon rikici
Yanzu haka manyan ƙasashen duniya sun fara mayar da martani a game da farmakin na Iran da kuma hasashen yadda hakan zai iya ƙara jefa yankin Gabas ta Tsakiya a cikin sabon rikici. Firaministan Faransa ya ce ya damu a game da wannan lamari, yayin da Jamus ta buƙaci Iran ta dakatar da hare-hare kan Isra’ila.
Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres, ya bayyana fargaba a game da wannan lamari, wanda a cewarsa ba abin da zai haifar face munanan halin da ake ciki a yankin da ya jima yana fama da rikice-rikice.
To sai dai ƙungiyar Hamas da Hezbollah suna jinjina wa Iran ne a game da irin martanin da ta mayar wa Isra’ila bayan asarar rayukan dubban mutane a Gaza da kisan manyan jami’an Hezbollah.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI