Iran da Amurka sun yi ɗamarar yaƙi bayan sabbin hare-haren Isra'ila a Lebanon

Iran da Amurka sun yi ɗamarar yaƙi bayan sabbin hare-haren Isra'ila a Lebanon

Hare-haren da Isra’ilan ta kai jiya su ne mafiya girma tun bayan faro farmakinta a Lebanon inda ta kashe mutane 37 tare da jikkata wasu 151 cikin ƙasa da sa'o'i 24 bisa alƙaluman ma’aikatar lafiya a Beirut, a ɓangare guda ta sake hallaka Falasɗinawa 18 a sansanin ƴan gudun hijira na Tulkarem da ke Gaza.

Wannan yaƙi ya sake ta’azzara ne tun bayan da Iran ta yi uwa da makarɓiya wajen farmakar Isra’ila da makaman roka har guda 200 wanda ta ce kashi 90 na hare-haren sun yi nasara a cikin Tel Aviv duk da cewa a baya-bayan nan ƙasar ta yi iƙirarin tare 180 da taimakon Amurka.

Bayan fitar wasu bayanai da ke nuna yiwuwar Isra’ilan ta farmaki sashen makamashi da man fetur ɗin Iran, tun a yammacin jiya Tehran ta aike da saƙon gargaɗi ga Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, dangane da abin da ka je ya zo matuƙar Isra’ila ta yi kuskuren kai mata hari.

A ɓangare guda masana tsaro irinsu Rami G Khouri da ya shahara wajen sharhin yanayin tsaron gabas ta tsakiya, ya koka da matakin sake girke ƙarin dakarun Amurka a yankin dama matakan da Amurkan ke ɗauka da sunan baiwa Isra’ila kariya wanda ya ce matakan na ci gaba da tsananta matsi ga Yahudawa tare da mayar da Isra’ila ƙasa mafi haɗari a ban ƙasa.

Khaouri ya bayyana cewa yanayin ɗamarar da Amurka ta yi a wannan karon ya nuna cewa ta shiryawa yaƙi da Iran batun da ya ce ba zai yiwa kowanne ɓangare daɗi ba.

Da sanyin safiyar yau ne wasu kafofin yaɗa labaran Isra’ila ke bayyana cewa hare-haren birnin Beirut a daren na jiya sun ritsa da Hashim Seifidden wato babban sakataren ƙungiyar Hezbollah wanda tun farko aka yi tsammanin ya maye gurbin ɗan uwansa Sayyed Hassan Nasrallah da Isra'ilan ta kashe.

Sai dai kawo yanzu Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa da ke nuna tabbacin ta kashe shi ba, saɓanin yadda ta saba a baya, haka zalika ƙungiyar ba ta sanar da kisan Seifidden ba, lamarin da ke nuna yiwuwar babu gaskiya a lamarin face farfaganda lura da cewa Hezbollah ba ta fiya muna-muna kan kashe mata mambobi ko shugabanni ba.

Yanzu haka dai Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare sassan Falasɗinu da Lebanon, Yemen da Syria baya ga Iran da ta ke ci gaba da shan alwashin farmaka, lamarin da ke nuna cewa Yahudawan ƙasar na iya fuskantar hare-hare daga kusan kowanne saƙo walau daga Mayaƙan Hamas ko Ansarullah ko Houthi a Yemen ko kuma ita ƙungiyar Hezbollar wadda ko a 2006 suka yi jina-jina a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)