Iraki ta tattauna da Turkiyya game da batun ruwa

Iraki ta tattauna da Turkiyya game da batun ruwa

Iraki ta sanar da kyakkyawan ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi da Turkiyya kan batun ruwa.

Sanarwar da Kakakin Ma'aikatar Albarkatun Ruwa na Iraki, Ali Samir ya fitar a Es-Sabah, jaridar gwamnati na cewa an kimanata jerin takardu game da tattaunawar da Turkiyya da Iraki suka yi kan ruwa.

Samir ya ce, Turkiyya ta jaddada cewa suna ba da muhimmanci ga kare hakkin Iraki na samun ruwa a kogunan da ke tsakanin kasashen biyu, kuma an samu ci gaba mai kyau a tattaunawar.

Kasar Iraki, wacce take samarda ruwan kasar musamman daga kogunan Tigris da Euphrates, tana fuskantar matsaloli wajen biyan bukatunta na ruwa na tsawon shekaru saboda raguwar ruwan sama.


News Source:   ()