Sojojin Iraki da na Peshmerga sun kaddamar da farmaki ta kasa kan kungiyar ta'adda ta DAESH a yankunan dake tsakanin lardin Diyala da Sulaymaniyah.
Runduna ta 52 a kasar Iraki da kuma reshen sojojin Peshmerga na 144 sun gudanar da wani farmaki daga wurare da dama a yankunan karkarar garin Zinane da ke gundumar Kifri na Sulaymaniyah inda Daesh ke fakewa.
An lura cewa a farmakin da aka gudanar da sanyin safiya, an kama manyan bindigogi mallakar kungiyar kuma an gano wasu ramukan da mambobin kungiyar ke labewa.
Labaran da kafafan yada labarai na cikin gida suka bayar na cewa, Italiya, wacce ke cikin kawancen yaki da Daesh, ita ma ta goyi bayan farmakan ta kasa tare da jiragen yaki.