Injin reactor mai amfani da makamashin nukilliya a Hadaddiyar Daular Larabawa

Injin reactor mai amfani da makamashin nukilliya a Hadaddiyar Daular Larabawa

Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa daya daga cikin injunan makamashin nukiliya 4 da aka gina domin biyan bukatun wutar lantarki a kasar yana aiki.

Mataimakin Shugaban kasa, Firaminista kuma Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktum, a cikin wata sanarwa da ya yada a shafinsa na Twitter ya ce,

"Ma'aikatanmu sun samu nasarar kammala aikin bayan sun cika mai kuma suka yi gwaji masu yawa." 

Maktum ya bayyana cewar burin su shi ne cewa duk injunan ba da wutar lantarki suyi cikakken aiki ta yadda za a iya biyan kashi 25 cikin 100 na bukatun wutar lantarki a kasar.

Tare da fara aikin injin reactor mai suna "Barakah", Hadaddiyar Daular Larabawa wanda ke da yawan mutane miliyan 9, ta zama kasar Larabawa ta farko da ta fara samar da wutar lantarki tare da karfin makaman nukiliya.

Hadaddiyar Daular Larabawa tana shirin ta mallaki injunan reactor 4, ciki har da Barakah nan da shekarar 2023. An bayyana cewar jimillar kudin zai kai dala biliyan 25.

 


News Source:   ()