Tun bayan saukar Southgate, kocin riko ne ke jagorancin kungiyar ta Ingila wadda ta sha kashi a hannun Girka a Wembley makon da ya gabata da ci 2-1 a gasar Nations League.
Tuchel mai shekaru 51 ba shi da aikin yi tun bayan raba garin da suka yi da Bayern Munich wadda ta maye gurbinsa da Vincent Komapany a karshen kakar da ta gabata.
Thomas Tuchel da Neymar lokacin da ya jagoranci PSG AP - Miguel A. LopesIngila na fatar ganin Tuchel ya fara aikinsa da kafar dama domin lashe mata kofunan da ta dade tana nema. Ana saran ya fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa.
Daga cikin manyan kungiyoyin da Tuchel ya jagoranta a nahiyar Turai akwai PSG ta Faransa da Chelsea ta Ingila da kuma Bayern Munich ta Jamus.
Makonni biyu da suka gabata, wasu rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutanen da Ingila ke zawarci, akwai Jurgen Klopp da Graham Potter da Eddie Howe.
Da wannan nadin Tuchel ya zama manaja na 3 wanda ba 'dan kasar Ingila ba da zai jagoranci kasar bayan Sven-Goran Eriksson da Fabio Capello.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI