Ingila ta amince da amfani da allurar riga-kafin Corona da kamfanin BioNTech na Jamus da daya daga cikin wadanda suka kafa shi Baturke Farfesa Ugur Sahin ne da kamfanin Pfizer na Amurka suka samar.
Tashar BBC ta bayyana cewar Hukumar Tabbatar da Ingancin Magunguna ta Ingila ta ce, babu matsala za a iya amfani da allurar riga-kafin Corona ta "BNT162b2".
Hakan ya sanya Ingila zama kasa ta farko da ta amince da wata allurar riga-kafin Corona da aka samar.
Bayan amincewar, a mako mai zuwa ake sa ran za a fara yin allurar riga-kafin a kasar.
A baya Ingila ta sanya hannu kan yarjejeniyar sayen allurar guda miliyan 40.
Wannan allura mai mRNA ta zama ta farko da aka amince da ita a duniya.
Cikin watanni 10 allurar ta samu nasarar amincewa bayan gwaji a dakunan bincike da gwada ta a kan mutane har a matakai 3.
BioNTech da Pfizer sun bayyana cewar allurar riga-kafin na samar da garkuwa ga dan adam da kaso 95 cikin dari.
Domin fara amfani da allurar ya sanya kamfanunnukan neman izini daga Hukumar Tabbatar da Ingancin Magunguna ta Turai da Hukumar Kula da Ingancin Abinci ta Amurka.
Kasashen Amurka, Kanada, Japan da na Turai da dama sun sanya hannu da kamfanunnukan don sayen alluran.
Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya bayyana cewar sun tattauna kan sayen alluran miliyan 25 inda a aatan Nuwamba za a ba su kwaya miliyan 1.
Kamfanin na da manufar samar da allurar guda miliyan 100 nan da karshen 2020, nan da karshen 2021 kuma zai samar da guda biliyan 1,3