Taron na bana da ke zuwa bayan makamancinsa da ya gudana a Rwanda cikin shekarar 2022 bayanai sun ce zai tattauna kan batutuwa masu alaƙa da tallafar rayuwar matasa biliyan 1 da rabi da nufin sauya musu rayuwa.
Gabanin faro taron na yau, wani batu da ya ja hankalin jama’a shi ne sanarwar gwamnatin Birtaniya da ke kawar da jita-jitar cewa Birtaniya na shirin amfani da damar taron wajen bayar da haƙuri kan abubuwan da suka faru a lokacin cinikin bayi.
Kakakin Downing Street a wata sanarwa da ya fitar, ya ce walau Sarki Charles ko Firaminista Keir Starmer da za su halarci taron babu ko guda cikinsu da zai bayar da haƙuri kan abin da ya faru a lokacin mulkin mallakar yayin cinikin bayi.
Jita-jitar yiwuwar baya da haƙuri yayin taron na bana ta ƙarfafa ne bayan wasu kalaman Sarki Charles yayin ziyararsa a Kenya cikin shekarar da ta gabata, inda ya bayyana nadama kan ɓarna da aka tafka da sunan cinikin bayi a lokacin mulkin mallaka, ko da ya ke tun a wancan lokaci bai bayar da haƙuri kan ɓarna da cin zarafin da Birtaniya da aikata kan baƙar fata ba.
Aƙalla shugabanni ko wakilan ƙasashe 56 ake saran su halarci wannan taro da ke gudana a Samoa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI