Indonesiya ta kame jiragen ruwa biyu da laifin fasa kwaurin mai

Indonesiya ta kame jiragen ruwa biyu da laifin fasa kwaurin mai

A kasar Indonesiya an tsare jiragen ruwan dakon mai biyu masu dauke da tutucin Iran da Panama da zargin fasa kwaurin mai.

A garin Pontianak ne dai jami'an tsaro suka dakatar da jiragen ruwan dakon man da suka keta iyaka ba bisa ka'ida ba.

An tabbatar da cewa mai ya rinka malala daga cikin jiragen da aka rufe sunayensu. Domin dai gudanar da bincike an kai jiragen yankin Batam.

 


News Source:   ()