Indiya ta hana yin amfani da manhajoji na waya guda 43, 4 daga cikinsu manyan kamfanonin kasuwanci ne na kasar China na Alibaba Group, bisa hujjar cewa ba su dace da tsaro da ikon mallakar kasar ba.
A cikin sanarwar da Ma’aikatar Kayan Lantarki da Bayanai ta fitar, an bayyana dalilan hana yin amfani da manhajojin da cewa “wadannan manhajojin na shiga cikin aiyukan da basu dace da mutuncin yankin Indiya ba da ikon mallakarta, tsaron kasa da tsarin jama’a.
Gwamnatin New Delhi ya hana yin amfani da manhajoji na waya da yawa a watannin Yuni da Satumba saboda dalilin tsarin tafiyar da mulkin Indiya.
Yawancin waɗannan manhajojin da aka hana amfani da suna da alaƙa da China.