An samu fiye da mutum miliyan biyu dauke da kwayar cutar Corona a kasar Indiya lamarin da ya sanya kasar a sahu na uku daga cikin kasashen da Covid-19 ta yi kamari bayan Amurka da Brazil.
A cikin kwanaki 20 ne kachal kasar ta samu karin yawan wadanda suke dauke da cutar daga miliyan 1 zuwa miliyan 2.
A cikin awanni 24 da suka gabata an samu karin mutum dubu 62,170 dauke da cutar a kasar lamarin da ya kara yawan masu dauke da cutar zuwa miliyan 2.03.Wadanda kuma suka rasa rayukansu sakamakon cutar sun kai dubu 41,638 a kasar.
Ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana cewa yawan samun wadanda ke warkewa kuma ya karu da kaso 67.62 cikin dari.