Ina kan bakata na sake fasalin tattalin arzikin Najeriya - Tinubu

Ina kan bakata na sake fasalin tattalin arzikin Najeriya - Tinubu

Shugaban wanda ya yaba da alakar Najeriya daFaransa, ya shaidawa shugaba Emmanuel Macron cewa babu gudu ba ja da baya kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara yi.

Da yake jawabi a wajen liyafar cin abincin dare da gwamnatin Faransa ta shirya masa a Palais des Elysée da ke birnin Paris a daren Alhamis, Tinubu ya karfafa gwiwar ‘yan Najeriya da Faransa da su ci gaba da kulla kyakkyawar alakar da kasashensu ke yi.

Tinubu ya ce Afirka ba ta da wani zabi illa gina nahiyar da za ta bunkasa fannoni da dama da suka kamata, da kuma inganta shirin walwalar jama’arta, yana mai nanata cewa gwamnatocin nahiyar sun himmatu matuka wajen inganta rayuwar al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)