Firayim Ministan Pakistan Imran Khan ya yi kira ga kasashen Turai da su hukunta duk wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW), suka ma yi amfani da irin wannan mizani domin hukunta wadanda ke yada maganganun kiyayya ga Musulmai da gangan.
Firaiministan Pakistan Imran Khan ya ce a cikin wata sanarwa a Twitter,
"A matsayinmu na musulmai, babban abin so da girmamawarmu shi ne Annabi Muhammad (SAW), wanda ya kasance zaune a cikin zukatanmu. (Ga Annabi Muhammad) ba za mu iya jure wa duk wani irin wannan rashin mutunci da cin mutunci ba."
Han dake jaddada cewa masu tsattsauran ra'ayi su nemi gafara daga al'umman Musulmi, ya kara da cewa,
"Wadanda ke Yammacin Turai, dake labewa karkashin inuwar 'yancin fadin albarkacin baki, gami da' yan siyasa masu tsattsauran ra'ayi wajen cin zarafin Musulmi, ba su da kwarin gwiwa da halin kirki na neman afuwa ga Musulmai biliyan 1.3 da suka ciwa mutunci."
Han, wanda ya yi kira ga kasashen Yammacin duniya da su haramta munanan kalamai akan addinin Islama a kasashensu, ya kara da cewa su yi kuma amfani da wannan mizanin wajen hukunta wadanda ke yada maganganun kiyayya ga Musulmai da gangan.