Imane ta shigar da kara saboda neman bata mata suna

Imane ta shigar da kara saboda neman bata mata suna

Hukumar kula ga wasannin Olympics ta duniya ta tabbatar da daukar matakin, sakamakon wallafa rahotan gwajin kwayoyin halittar da aka yiwa Imane wadda wasu ke zargin cewa ba mace bace.

Rikicin jinsin Imane ya bayyana lokacin da ta doke abokiyar karawarta Angela Carini 'yar kasar Italia a cikin dakika 46 da fara damben.

Imane Khelif Imane Khelif AFP - MOHD RASFAN

Carini cikin hawaye ta ruga ta fice daga filin damben inda take cewa abokiyar karawarta ba mace bace, saboda zafin naushin da ta ji daga hannunta, abinda ya kai ga ta samu rauni a hancinta.

Wannan matsala ta kai ga sanya bakin manyan 'yan siyasar kasashen biyu ciki harda Firaminista Giorgia Meloni.

Hukumar kul ada wasannin Olympcs ta ce ta samu labarin karar da Imane ta shigar kuma ta shirya na ta ba'asin da za ta gabatar a kotun.

Hukumar IOC ta ce Imane ta shiga wasanni daban daban a karkashin hukumar dambe ta duniya cikinsu harda wasannin Olympics na Tokyo a shekarar 2021 da gasar damben duniya daban daban kafin wasannin na Paris, kuma babu wanda ya taba korafi a kanta.

 Imane Khelif a garin su na Tiaret Imane Khelif a garin su na Tiaret AFP - -

Hukumar wasannin tace abin takaici ne yadda ake cin zarafin Imane saboda yanayin halittara ta.

Bayan kammala gasar Olympics da aka yi a Paris, Imane ta samu kyakyawar tarbo a kasar Algeria lokacin da ta koma gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)