Iƙirarin ƙwace Gaza - Amurka ta yi amai ta lashe

Iƙirarin ƙwace Gaza - Amurka ta yi amai ta lashe

Kalaman na Trump dai sun fuskanci zazzafar suka daga Falasɗinawa da gwamnatocin ƙasashen Larabawa da kuma shugabannin ƙasashen duniya, lamarin da ya sa sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya ce ba wai ƙwace yankin Gaza baki ɗaya Trump zai yi ba, za a kwashesu Falasɗinawa ne na wucin gadi don bada damar share ɓuraɓuzan da ke yankin.

Abin da ya ke nufi shi ne, kwashe Falasɗinawa daga yankin zai bai wa Amurka dama wajen kawar da ɓuraɓuzai da kwance nakiyoyi, da kuma taimakawa wajen sake gina gidaje da kasuwanni da abubuwan more rayuwa, ta yadda mutane za su koma gidajensu.

Ita ma dai kakakin fadar White House Karoline Leavitt, ta ce ba a fahimci kalaman Trump ba ne, abinda ya ke nufi shi ne nema wa Falasɗinawa matsugunni na wucin gadi, don sake gina yankin na Gaza.

Ta kuma ce babu wani ƙuduri da Amurka ke da shi, na tura sojojinta yankin Gaza.

Bayan kalaman na Trump dai, tarin ƙasashe ne suka mayar da martani, inda ƙasashen irin Saudiya da Jordan da kuma Iran, ke bayyana matakin a matsayin ba mai yiwuwa ba, tare da sake nanata fatan samar da ƙasashe biyu na Falasɗinu da Isra’ila, a matsayin maslaha ga rikicin yankin.

Ita ma Hukumar Kula da Yankin na Falasɗinu ta PLO da Hamas da kuma Islamic jihad, sun gargaɗi manyan hukumomin duniya kan illar da wannan alwashi na Trump ka iya haifarwa, bayan da suka bayyana cewa sai dai shugaban na Amurka ya yi amfani da ƙarfi wajen aikata kisan ƙare dangi ga al’ummar ta Gaza gabanin iya karɓarsa, lura da cewa Falasɗinawa baza su bar matsugunansu ba, kuma hatta a yankunan da Isra’ila ta rusa musu za su ci gaba da koma wa gidajensu.

Ƙungiyar Ƙasashe Musulmi ta IOC ta bi sahun ƙasashen Saudiya da Jordan da kuma Iran, waɗanda cikin sauri suka yi tir da alwashin na Trump kan Gaza, tare da bayyana matakin a matsayin wanda ba zai yiwuwa ba.

Sauran ƙasashen da suka yi kakkausar suka kan kalaman na Trump sun ƙunshi Birtaniya da Jamus da China da Turkiya da Spain da Faransa da Brazil da Masar da Rasha da Ireland da kuma Australia.

Haka nan ƙungiyoyi irin Majalisar Ɗinkin Duniya da Amnesty International da Human Right Watch, sun yi tir da kalamansa kan yankin na Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)