IFRC: Dole a yaki yada bayanan karya don magance yaduwar Corona a duniya

IFRC: Dole a yaki yada bayanan karya don magance yaduwar Corona a duniya

Tarayyar Kungiyoyin Red Cross da Red Crescent (IFRC) ta bayyana cewar, matukar ana son a yaki yaduwar cutar Corona yadda ya kamata, to dole ne a yaki yada bayanan karya.

Tarayyar ta yi gargadi da cewar, allurar riga-kafi kadai ba za ta yaki cutar Corona a duniya ba.

A wajen wan, taron manema labarai da Shugaban IFRC Francesco Rocca ya gudanar ya ce

"Riga-kafi kadai ba za ta yi maganin yaduwar cutar Corona ba. Idan muna son mu yaki cutar Covid-19 baki daya, dole a gwagwarmayar da muke yi mu yaki yada bayanan karya da bogi da rashin tsaro da aminci."

Rocca ya ja hankali kan wani bincike da Jami'ar John Hopkins ta gudanar wanda ya gano cewar, a kasashen duniya 67 amincewar da mutane suka yi wa allurar riga-kafin Corona ya ragu sosai.

Ya ce a kasashen Afirka ana yi wa Covid-19 kallon wata matsala ce da ta shafi Yammacin Duniya kawai.

Roca ya ci gaba da cewar, a Yammacin Duniya kuma mutane da yawa na kin amincewa da allurar saboda ta sabawa yanayin lafiyarsu, a saboda haka dole ne gwamnatoci su tashi tsaye wajen yaki da bayanan karya da ake yadawa game da riga-kafin Corona.

 


News Source:   ()