Ɓangarori da dama ne dai kama daga shugabannin manyan hukumomi, da na ƙasashe suka mayar da martani kan matakin kotun ICC.
Ƙungiyar ƙasashen Turai EU ce ta baya bayan nan da ta yi tsokaci akai, inda babban jami’in diflomasiyyarta Joseph Borrel yayi kira da a yi biyayya a kuma aiwatar da umarnin kotun duniyar, domin a cewarsa babu siyasa ko rufa-rufa cikin sammacin da ta bayar.
Daga bangaren Isra’ila kuwa Fira Minista netanyahu da ke cikin waɗanda ICCn ta ce a cafko, bayyana umarnin yayi a matsayin tsantsar nuna ƙiyayya ga Yahudawa. Shi kuwa shugaban Isra’ila bayyana wannan rana yayi a matsayin baƙa da ‘yancin ɗan Adam, yayin da shi kuma jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya kira sammacin na ICC a matsayin “goron kyauta ga ta’addanci”.
Daga Gabas Ta Tsakiya, Jordan ce ta fara tsokaci, inda ministan harkokin wajen ƙasar Ayman Safadi ya ce ya zama dole a mutunta umarnin kamen da kotun ICC ta bayar, ya kuma ƙara da cewar Falasɗinawa sun cancanci bi musu hakkin uƙubar da Isra’ila ke yi musu Gaza.
A nata ɓangaren Faransa ta ce a halin yanzu nazari take yi akan tasirin da umarnin ICC na a kamo mata Fira Ministan Isra’ila zai yi ta fuskar shari’ah. A lokacin kuma da manema labarai suka tambayi kakakin ma’aikkatar wajen Faransar Christophe lemoine kan ko Faransa za ta cafke Netanyahu idan ya sanya kafa cikin ƙasar, sai ya noƙe wajen bayar da amsar, tare da cewa akwai sarƙaƙiyar shari’ah a tattare da hakan.
Sai dai ƙasar Netherlands ko Holland ba ta ɓata lokaci ba wajen bayyana cewar a shirye take ta cafke dukkanin mutanen da kotun duniyar ta buƙaci a kama mata su da zarar ta samun damar hakan.
Ya zuwa yanzu yawan waɗanda suka rasa rayukansu a Zirin Gaza ya zarce mutane dubu 44,000, yayin da wasu aƙalla dubu 104 da 268 suka jikkata, tun bayan fara ruwan bama baman da Isra'ila ta fara kan yankin na Gaza, da zummar ɗaukar fansar hare-haren ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da mayakan Hamas suka kai tare da halaka mata mutane fiye da dubu 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI