ICC na bukatar goyon bayanmu game da hukuncin kama Netanyahu - G7

ICC na bukatar goyon bayanmu game da hukuncin kama Netanyahu - G7

Ministan harkokin wajen Italiya, Antonio Tajani wanda ya bayyana hakan a taron kungiyar da ya gudana a kasarsa, ya ce akwai bukatar kasashe mambobin G7 su bawa ICC hadin kai wajen aiwatar da wannan hukunci nata.

Kasar Amurka wadda ta kasance guda daga cikin mambobin kungiyar, ta yi watsi da matakin ICC, inda shugaba joe Biden ya bayyana matakin kotun a matsayin zalunci.

Tajani, wanda ya kasance cikin ministocin kasashen kungiyar da suka halarci taron, ya ce akwai bukatar G7 ta kasance mai magana guda, ba wai samun rarrabuwar kawuna kan abin da yake a bayyane ba.

A makon jiya ne, kotun ICC ta fitar da sanarwar kama Netanyahu, tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant da kuma jagoran Hamas, Ibrahim Al-Masri, bisa zarginsu da aikata laifukan yaki a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)