Sakataren Ma’aikatar Tsaron Hungary, Gaspar Maroth ya bayyana cewar kasarsa ta sayi karin motoci masu sulke 40 daga Turkiyya.
Maroth ya bayyana wa Kamfanin dillacin labarai na Hungary (MTI) cewa suna da niyyar sayen motoci masu sulke sama da 300 tare da shirin da aka tsara don kara karfin tsaro na sojoji.
Maroth ya ce sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da Turkiyya a karkashin shirin don samar da karin motoci 40 masu sulke samfurin 4x4.
Hungary ita ce ta 6 a duniya kuma kasa ta farko a Tarayyar Turai da ta zabi Ejder Yalcin don biyan bukatun jami'an tsaro.