Kotun kolin Turai ta yanke hukuncin cewa masu daukan mutane aiki na iya haramta wa ma’aikata sanya lullubi saboda wasu dalilai.
Kotun ta kammala shari’ar hana sanya lullubi da wasu mata musulmai biyu suka shigar a kasar ta Jamus.
A cikin hukuncin, an lura da cewa hana sanya lullubi wani hanya ne na hana nuna son kai ga kwastomomi da kuma hana nuna bambancin jama’a.
Daya daga cikin matan da suka shigar da kara ta yi aiki a wata cibiyar kula da yara masu zaman kansu da wata gidauniya ta dauki nauyinta, dayar kuma ta yi aiki a wani shagon sayar da kayan masarufi.