Hukuncin karin shekaru 4 ga wani Bafalasdine da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai

Hukuncin karin shekaru 4 ga wani Bafalasdine da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai

Kotun Isra'ila ya ba da hukuncin karin shekaru 4 ga wani Bafalasdine da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai a baya.

A cikin rubutacciyar sanarwar da Kwamitin Fursunonin da ke da alaka da Kungiyar ‘Yantar da Falasdinawa ta fitar, an bayyana cewar Kotun Salim ta Soji da ke yankin Yammacin Gabar Kogin da ke karkashin mamaya ya ba wa dan gidan yari Bafalasdine, Yusuf Halid Kumeyl karin shekaru 4 bayan hukuncin da aka yanke masa na daurin rai da rai a baya.

A cikin sanarwar an bayyana cewar Kumeyl wanda aka yanke wa hukuncin kisan wani dan Isra’ila ya kasance a kurkuku tun shekarar 2017, an gabatar da sabbin tuhume-tuhume a kan Kumeyl ga kotun kuma an yanke sabon hukuncin a kan hakan.

Dangane da bayanan hukumomin Falasdinu, akwai ‘yan kasar Falasdinu kusan 4,500 a gidajen yarin Isra’ila.


News Source:   ()