Hukumomi sun tabbatar da cewa guguwar Chido ta hallaka mutum 70 a Mozambique

Hukumomi sun tabbatar da cewa guguwar Chido ta hallaka mutum 70 a Mozambique

Sabbin alƙaluman da hukumar kula da annoba ta Mozambique ta fitar a ranar Laraba sun tabbatar da cewa guguwar Chido mai ƙarfin gaske ta kashe a ƙalla mutum 70.

Wannan bala’in guguwa ya sanya mutane afkawa cikin garari a arewacin Mozambique kamar yadda ya jefa yankin Mayotte. Sai dai masu ayyukan ceto na da shakku kan alƙaluman.

Hukumomi a Maputo sun ce mahaukaciyar guguwar ta shafi sama da mutum dubu 180. Ana kuma ci gaba da ƙoƙarin gano ainahin ɓarnar da guguwar ta yi a kwanaki 4 bayan wucewar da guguwar ta chido ta yi.

Shugaban mozambique mai barin gado Filipe Helpe ya ce tuni suka aika da kayan agaji zuwa yankunan arewacin ƙasar da guguwar tafi yiwa ɓarna kamar Nampula, Niassa da Cabo Delgado.

Hukumar samar da abinci ta majalisar ɗinkin duniya ta ce yankin Mecufi ya ɗaiɗaice kuma mutane dubu 67 na buƙatar agajin gaggawa a lardin Cabo Delgado da bai jima da fara farfaɗowa daga yaƙin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da masu iƙirarin jihadi.

A ziyarar da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai yankin Mayotte ya sanar da ranar litinin mai zuwa a matsayin ranar hutu  domin jimamin ɓarnar da guguwar ta haddasa.

Firaministan Faransa Farancois Bayrou ya ce guguwar ta chido ita ce annoba mafi muni da Faransa ta fuskanta dubban shekaru da suka gabata. Mutane 31 ne suka mutu a yankin na Mayotte sai dai ana fargabar adadin ka iya ƙaruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)