Gwamnan jihar Guerrero, Evelyn Salgado, a wani sako da ta wallafa a shafinta na sada zumunta bayan kisan gillar ɗan siyasar, ta ce sun fusata matuƙa game da kisan Alejandro Arcos da aka yi, sai dai bata yi ƙarin haske kan lamarin ba.
Kafofin yada labaran ƙasar sun ruwaito cewa an datse kan Arcos ne, duk da cewa babu wani tabbaci a hukumance game da hakan.
Ita dai jihar Guerrero na ɗaya daga cikin jihohin Mexico da suka fi fama da talauci, kuma tana fama da matsalolin tsaro cikin shekarun baya-bayan nan, wanda ya danganci rikicin da ake yi tsakanin masu fataucin miyagun kwayoyi.
A shekarar da ta gabata kadai, mutane dubu ɗaya da dari 890 ne aka kashe a jihar.
Sama da mutane dubu dari 450 ne aka kashe a bara a duk faɗin ƙasar ta Mexico, yayin da dubbai suka ɓace bayan da a shekarar 2006, gwamnatin ƙasar ta tura sojoji domin yaki da safarar miyagun kwayoyi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI