Hukumar WHO ta jinjinawa Turkiyya akan yaki da Covid-19

Hukumar WHO ta jinjinawa Turkiyya akan yaki da Covid-19

Ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta Nahiyar Turai ta yaba tare da jinjinawa Turkiyya akan matakan da take dauka na dakile kwayar cutar Covid-19 akan yadda kasar ta kara yawan wadanda ake yiwa gwajin cutar har sau uku a rana tun daga watan Agusta kawo yanzu.

Ofishin WHO a yankin Turai ta fitar da wata sanarwa akan wadanda ke bin dokar da aka tsara akan dakile kwayar cutar Covid-19. Inda ta bayyana cewa,

"Abin yabawa ne da koyi akan yadda Turkiyya ta kara daukar matakan dakile cutar ta hanyar kebe wadanda suka nuna alamu da kuma kara yawan gwajin da ake yi a ranar wanda kasar ta ribiya sau uku a watan Agusta."

Sanarwar ta kara da cewa irin yadda Turkiyya ta dauki matakan gano da kebe wadanda suka nuna alamun kamuwa da kwayar cutar ta Korona da kuma kebe wadanda suka kamu da ita abu ne abin koyi da yabawa.

Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dtk. Fahrettin Koca,  ya yada a shafinsa ta Twitter inda ya mika godiya ta musanman ga ofishin WHO na yankin Turai akan yabawa Turkiyya da ta yi na kwararan matakan da take dauka a dakile kwayar cutar Korona.

 


News Source:   ()