Mai magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO Dkt. Margaret Harris ta yi sharhi akan taimakawa kasashe fiye da 80 da Turkiyya ta yi da kayayyakin kiwon lafiyar yaki da kwayar cutar Covid-19.
Ta bayyana cewa "Wannan taimakon misali ne da darasi mai kyau mai inganci abin koyi"
Mai magana ya yawun Hukumar WHO wacce kwararriya ce a shashen epidemiology- ilimin kare yaduwar cututtuka Dkt. Margaret Harris ta yi wannan sharhin ne ga kanfanin dillancin labaran Anadolu.
Harris, ta bayyana cewa wannan mataki na Turkiyya na taimakawa fiye da kasashe 80 da kayayyakin taimako abin yabo ne kuma abin so da koyi.
"Wannan taimakon kekkyawar hali ce a gurin taimakwa wajen kauda wacanan kwayar cutar corona da ke cigaba da abbadar duniya."
Turkiyya ta taimakawa kasashen Amurka, Ingila, Italiya da kasashen Balkan da Afirka da sauran kasashe da dama da kayayakin taimakon yaki da Covid-19
Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu a jawabin da ya yi a ranar 15 ga watan Mayu ya bayyana cewa kasashe 135 suka nemi taimakon kayayyakin kiwon lafiya daga Turkiyya daga cikinsu Turkiyyar ta taimakawa fiye da kasashe 80.