Hukumar kula da ilimim kananan yara ta MDD UNICEF ta bayyana cewa, Wani sabon rahoto ya nuna cewa sama da yara miliyan 500 ne ‘yan kasa da shekaru biyar a duniya aka yiwa rajista a lokacin haihuwarsu a cikin shekaru biyar da suka gabata.
Rahoton hukumar ta UNICEF ya nuna cewa an samu gagarumin ci gaba a kokarin da kasashen duniya ke yi na tabbatar da kokarin yara.
Rahoton mai taken "Farkon Dama a Rayuwa: Matsayin Duniya da Tattalin Arziki a cikin Rijistar Haihuwa" ya nuna cewa duk da karuwar yawan yaran da ake yi wa rijista, kimanin yara miliyan 150 har yanzu ba su samu rajista ba.
Ya kuma yi nuni da cewa sama da yara miliyan 50 da ke da rijistar haihuwa ba su da takaddun haihuwa wanda wanda ke da muhimmanci don tabbatar da shaida bisa doka da samun asalin ƙasa, da samun damar kiwon lafiya, ilimi, da kuma kariya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI