Hukumar samar da abinci ta Majalisar dinkin duniya ta ce yanzu haka motocin dake dauke da kayan abinci sun far shiga Gaza ta hanyar Zikim da Kerem.
Bayanai sun ce motocin farko da suka fara shiga Gazar na dauke ne da kayan abincin gaggawa da kuma buhunan fulawa domin sarrafawa ga mabukata.
Wasu Falasdinawan dake murnar kawo karshen yakin da aka yi AFP - BASHAR TALEBHukumar samar da abincin ta ce a shirye take ta ci gaba da shigar da kayan abincin ta iyakokin Masar da Jordan da kuma Isra'ila domin kai dauki ga mutanen da yunwa ya taggayara a yankin.
Irin mummnar yanayin da mutanen Gaza suka shiga na rashin abinci ya sanya gindaya sharadin kai daukin abinci cikin manyan kudirorin da bangarorin biyu dake yaki suka amince da su.
Rahotanni sun ce mazaunan yankin Gaza da dama sun taggayara sakamakon yunwa da rashin tsaftacacen ruwan sha, yayin da wasu da dama ke fama da rashin lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI