Hukumar FBI na gargadi dangane da masu yada labaran karya

Hukumar FBI na gargadi dangane da masu yada labaran karya

Wannan na daga cikin labaran karya da ake amfani da su domin hana jama'a fitowa kada kuri'u a wasu sassan kasar.

Daya daga cikin bidiyon da ake cewa ya fito ne daga hukumomin tsaron Amurka ya bukaci jama'a da su yi taka tsan tsan dangane da kare lafiyarsu wajen zabe, yayin da wani kuma ya bayyana shirin magudi a gidajen yarin kasar guda 5.

Hukumar FBI ta bayyana wadannan bidiyo guda 2 a matsayin marasa sahihanci da ake so ayi amfani da su domin razana jama'a masu kada kuri'a da kuma yiwa zaben kasdar zagon kasa.

Hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi na ta gargadin jama'a akn yunkurin wasu batagari na yada labaran karya domin jefa shakku da kuma tababa dangane da zaben na Amurka.

Rahotanni sun ce ya zuwa karfe 2 na ranar yau Talata a gogon Amurka babu wata matsala da aka fuskanta dangane da zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)