Hukumar FBI na ci gaba da gudanar da binciken harin da aka sake kaiwa Trump

Hukumar FBI na ci gaba da gudanar da binciken harin da aka sake kaiwa Trump

A cewar Hukumar ta FBI, bayan harba bingidar da maharin ya yi, ya yar da ita ya kuma hau mota da nufin ya tsere wa daga wajen, sai dai da taimakon wani wanda ya shaida faruwar lamarin, sun samu nasarar kama wanda ake zargin kuma ana nan ana ci gaba da gudanar da bincike kan sa.

Wannan dai shi ne hari na baya-baya da aka kaiwa tsohon shugaban ƙasar ta Amurka Donald Trump, domin watanni biyu da suka gabata anyi yunkurin hallakashi a lokacin yaƙin neman zabe a Pennsylvania, inda alburushi ya goge shi a kunne.

Tun daga wancan lokacin ne kuma tsohon shugaban ƙasar na Amurka ya ƙara tsaurara matakan tsaron da ke bashi kariya.

Tuni dai fadar White House ta ce shugaban ƙasar Joe Biden da kuma mataimakiyarsa kuma ƴar takarar jami’iyar Democratic Kamala Harris, suka jajanta masa bisa faruwar iftila’in.

A wata sanarwa da Harris ta fitar ta ce abin farin ciki ne yadda Allah ya kare Trump daga wannan hari, sannan ta ce tashin hankali ba zai samu matsugunni a Amurka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)