A lokacin da Naim Qassem ke gabatar da jawabi kai tsaye a kafar talabijin, ya ce hanya daya tilo da za a kawo ƙarshen wannan rikici ita ce cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, amma a cewarsa hare-haren da Isra’ila ke kai musu ba zai razanasu ba.
To sai dai a yayin wata ganawa da aka yi tsakanin faraministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da shugaba Emmanuel Macron na Faransa a jiya Talata, ya shaida masa cewa ba zai amince da duk wata yarjejeniyar tsagaita wutar da ba za ta dakatar da Hezbullah wajen sake samun ƙarfinta ba.
Isra'ila dai na ƙara zafafa kai hare-hare kan mayaƙan ƙungiyar Hezbullah, tun bayan kashe shugabanta Hassan Nasrallah da kuma wasu kwamandojin a watan da ya gabata.
Kawo yanzu dai, Hukumar da ke Kula da Ƴan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce Isra’ila ta baiwa kaso ɗaya bisa hudu na al’ummar Lebanon umarnin barin muhallansu, tare da shan alwashin ci gaba da kai hare-hare kowane ɓangare na ƙasar ciki har da birnin Beirut.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI