Hezbollah ta tabbatar da mutuwar jagoranta Nasrallah a harin Isra'ila

Hezbollah ta tabbatar da mutuwar jagoranta Nasrallah a harin Isra'ila

Kisan Nasrallah na matsayin babban koma baya ga ƙungiyar mai samun goyon bayan Iran wadda kuma ta shafe tsawon lokaci ta na yaƙi da Isra’ila, ƙasar yahudawa ɗaya tilo da ke tsakankanin ƙasashen gabas ta tsakiya masu rinjayen musulmi.

Tun gabanin sanarwar kisan Nasrallah daga Hezbollah, ƙasashen yammaci da ke matsayin manyan ƙawayen Isra’ila ciki har da Faransa sun bayar da tabbacin kisan jagoran baya ga wani babban janar ɗin dakarun juyin juya halin Iran da shima Isra’ilan ta hallaka a Beirut.

Bugu da ƙari kisan na Nasrallah babban koma baya ne ga Iran wadda ke matsayin babbar mai taimakawa ƙungiyar ta kusan kowacce fuska.

Sanarwar da Hezbollah ta fitar ta ce ayyukanta za su ci gaba, haka zalika yaƙinta da Isra’ila don baiwa Lebanon da al’ummarta kariya.

Duk da cewa sanarwar ta Hezbollah ba ta yi cikakken bayani kan yadda Isra’ila ta kashe Nasrallah ba, amma ta sha alwashin ci gaba da yaƙar da ƙasar.

Gidan talabijin na AL-Manar mallakin Hezbollah da ya sanar da mutuwar Sayyed Nasrallah ya ci gaba da haska karatun Qur’ani mai girma don jimama mutuwar jagoran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)