Henry ya sanar da matakin da ya dauka ne yau litinin bayan ya taimakawa kasar lashe azurfar gasar Paris Olympics da ya gudana.
Tsohon fitaccen 'dan wasan Arsenal dake rike da matsayin 'dan wasan da ya fi kowa zirarawa kungiyar kwallaye, ya karbi aikin horar da matasan Faransar ne bara, inda ya rattaba hannu a kwangilar shekaru 2 da zata kai shi har zuwa watan Yunin shekara mai zuwa, amma sai ya bayyana cewar zai aje mukamin saboda wasu dalilai na kashin kansa.
Tawagar 'yan wasan sa sun sha kashi da ci 5-3 a karawar da suka yi da kasar Spain wadda ta lashe zinaren gasar, a lokacin da ya fuskanci kalubale wajen rashin samun wasu daga cikin 'yan wasan da yake bukata daga kungiyarsu, cikin su harda Kylian Mbappe.
Henry ya jinjinawa Hukumar kwallon kafar kasar da kuma shugaban ta Philippe Diallo saboda damar da suka ba shi, ya yin da ya bayyana lashe azurfar kwallon kafar a matsayin daya daga cikin abubuwan da ba zai manta ba a rayuwarsa.
Diallo ya yabawa Henry saboda rawar da ya taka da kungiyar matasan, ya yin da ya bayyana bakin cikin su na rabuwa da shi.
Ya zuwa babu wani labari dangane da inda zai koma aiki, ya yin da wasu ke hasashen cewar mai yiwuwa ya karbi wata kungiya a nahiyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI