Hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a Faransa

Hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a Faransa

Mutane 2 sun mutu, wasu 3 sun jikkata sakamakon fadowar jirgin sama mai saukar ungulu a a yankin Courchevel da ake wasan kankara a kudancin Faransa.

Sanarwar da aka fitar daga fadar gwamnan Savoie ta ce, jirgin saman ya tashi dauke da mutane 5 da misalin karfe 17.00 inda ya fado a kewayen Tsaunin Charvet.

Sanarwar ta ce, an aike da jami'an ceto ta hanyar taimakon da shaidun gani da ido suka bayar, kuma harin ya afku a tudu mai tsayin mita 1900.

An bayyana mutuwar mutane 2 da jikkatar wasu 3 sakamakon hatsarin.

A watan Disamban bara a wannan yankin na Faransa mutane 5 sun mutu sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu.


News Source:   ()