Za a biya iyalen wadanda suka rasa rayukansu a jirgin saman fasinja na Kamfanin Sriwijaya da ya yi hatsari a Indonesiya a ranar 9 ga watan Janairu, diyyar dala dubu 92 da 660 kowannensu.
Shugaban Indonesiya, Joko Widodo ya ziyarci Cibiyar Kula da Rikicin Hatsarin Jirgin Saman a yankin tashar jiragen ruwa a Jakarta, babban birnin kasar.
Da Widodo ke yin jawabi a can, ya bayyana cewar za a biya iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a cikin hatsarin.
Ya bayyana cewar Kamfanin Jirgin Sama na Sriwijaya zai biya rupiah biliyan 1.25 (dala dubu 89 da 100) ga 'yan uwan fasinjojin da suka mutu. Widodo ya kuma ce kamfanin inshora mallakar Jasa Raharja zai ba da rupiah miliyan 50 (dala dubu 3 da 560).
Widodo ya gode wa dukkan cibiyoyin da ma’aikatan da suka gudanar da aiyukan bincike da ceto bayan hatsarin.
Yayin da ake ci gaba da neman abun da ya bace a akwatin injin din cikin jirgin, sai aka gano wani akwatin injin na waje, batir da na'urar sigina da daukar murya a ranar 15 ga Janairu.
Kwamitin Tsaro na Sufurin Kasa (KNKT), a cikin sanarwar da ya fitar a jiya, ya bayyana cewar ana bincike kan bayanan da ke cikin akwatin inji na farko da aka cire daga jirgin a ranar 12 ga Janairu kuma za a sanar da rahoton farko na dalilin hatsarin nan da kwanaki 30.
A taron manema labarai da aka gudanar a ranar 9 ga Janairu, Ministan Sufuri, Budi Karya Sumadi ya bayyana cewar jirgin fasinjan samfurin Boeing 737-500 mai lamba "SJ182", dauke da fasinjoji 50 da ma'aikatan jirgin 12, ya fadi tsakanin Laki da ke arewacin babban birnin kasar, Jakarta da Tsibirin Lancang bayan sadarwa ta katse kusan minti 5 kacal bayan tashinsa.