Mutane 6 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar wani jirgin sama a kudu maso-yammacin Port-au-Prince Babban Birnin Haiti.
Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, jirgin ya tashi da yammacin Lahadin nan daga birnin Port-au-Prince zuwa garin Jamel na kudancin kasar.
Babu wanda ya tsira daga cikin mutane 6 da ke cikin jirgin.
Ba a san musabbabin fadowar jirgin ba, an kuma fara gudanar da bincike.